in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faraministan kasar Sin ya isa Faransa
2015-06-30 11:14:48 cri

Faraministan kasar Sin Li Keqiang ya isa Paris a ranar Litinin da yamma a wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu a kasar Faransa.

Wannan ita ce ziyara ta farko da wani faraministan kasar Sin ya kai a kasar Faransa tun bayan kimanin shekaru goma da suka gabata.

A yayin wannan rangadi, mista Li zai ziyarci wasu biranen kasar Faransa da suka hada da Paris, Marseille da Toulouse, kuma zai gabatar da wani jawabi a cibiyar kungiyar dangantaka da tattalin arziki ta OCDE, kafin kuma ya halarci bikin rufe dandalin harkoki tsakanin Sin da Faransa.

Firaministan gwammnatin kasar Sin zai gana kuma da shugaban kasar Faransa Francois Hollande, faraministan kasar Manuel Valls, shugabannin majalisar dattawa da na majalisar dokokin kasar Faransa, sakatare janar kungiyar OCDE da kuma darektar janar kungiyar UNESCO.

Haka kuma a yayin wannan ziyara ta faraministan kasar Sin, kasashen Sin da Faransa za su daddale wasu jerin kwangilolin kasuwanci da yarjejeniyoyin gwamnatocin biyu musammun ma a bangarorin sufurin jiragen sama, kudi, makamashin nukuliya na jama'a, da kuma dangantaka kan kausuwanni masu tasowa.

Ziyarar Li a kasar Faransa dai, ta biyu bayan ziyarar tahiri da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai a kasar Faransa a cikin watan Maris din shekarar 2014, domin martaba cikon shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa, inda a yayin wannan ziyara bangarorin biyu suka cimma ra'ayin kara daga dangantakarsu zuwa wata huldar cin moriyar juna cikin karko.

A cewar wasu alkaluman Tarayyar EU, adadin musanyar kasuwanci tsakanin Sin da Faransa ya cimma dalar Amurka biliyan 55 a shekarar 2014, wanda ya karu da kashi 5,3 cikin 100 idan aka kwantanta na da shekarar da ta gabata.

A yanzu haka, kasar Sin ta kasance kasuwa ta takwas wajen fitar da kayayyaki zuwa Faransa, kuma ta shida wajen shigo da kayayyaki.

Ziyarar mista Li ta zo daidai da lokacin da kasar Sin da OCDE suke bikin cikon shekaru 20 da kulla huldar dangantakarsu, kuma za ta taimakawa OCDE wajen fahimtar matsayin kasuwanni masu tasowa da kasashen da ke neman ci gaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China