Jami'an tsaron kasar Nijar na (FDS) sun cafke wasu mambobin kungiyar Boko Haram tare da kubutar da wasu mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su a cikin jihar Bosso dake kuriyar gabashin kasar Nijar mai iyaka da Najeriya, a wani labarin da gidan rediyo Anfani mai zaman kansa ya bayar a ranar Laraba, da yake ambato majiyoyin jami'an tsaro.
Mayakan Boko Haram sun kai hari a cikin daren ranakun 15 zuwa 16 ga watan Junin da ya gabata a yankin kasar Nijar na Balankoiri a cikin jihar Bosso, tare da kashe wani mazaunin kauyen guda da kuma sace wasu matasa biyu, in ji rediyon. (Maman Ada)