Wannan ne karo na biyu da Mozambique ta kai ga wasan karshe na wannan gasa, tun bayan halartar ta wasan na karshe a shekarar 2008, lokacin da ta doke Afirka ta kudu da ci 2 da 1.
Da yake tsokaci game da hakan, kocin kungiyar ta Mozambique Joao Chissano, ya ce sun shirya tsaf domin lashe wannan wasa na karshen mako. Chissano ya kara da cewa 'yan wasan sa na cikin kyakkyawan yanayi da zai basu nasarar da suke bukata, duk kuwa da kwararrun 'yan wasa da kasar Namibia ke da su.
Ya ce za a kai-ruwa-rana a wasan na ranar Asabar, duba da cewa abokan hamayyar su ba za su bada dama ga Mozambique ta dauki kofin cikin sauki ba, amma duk da haka yana cike da kyakkyawan fatan samun nasara.
Kafin dai kaiwa ga wasan na karshe, sai da Mozambique ta doke Malawi, wadda a baya aka rika zatawa samun nasarar daukar kofin na COSAFA, da kuma kulaf din kasar Botswana, wanda shima Mozambique din ta doke da ci 2 da 1 a wasan su na birnin Rustenburg.
Kulaf din kasar Mozambique wanda ake kira da Mambas ya gudanar da wasan atisaye a ranar Juma'a gabanin wasan dake tafe a ranar Asabar.
A wani ci gaban kuma, shugaban kasar ta Mozambique Filipe Nyusi, shima ya bayyana fatan nasara ga kungiyar kasar ta sa, yana mai burin ganin Mozambique din ta dau kofin na COSAFA na bana.(Saminu Alhassan)