in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kasashen Afirka za su amfana da tallafin bankin duniya
2014-10-28 09:51:10 cri

Bankin duniya ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba wasu kasashen Afirka guda 8 dake yankin kusurwar Afirka za su amfana da wani tallafin raya kasa na dala biliyan 8 da masu bayar da agaji suka bayar.

Wata sanarwa da ofishin bankin da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya ya bayar a ranar Litinin ta bayyana cewa, kasashen da za su amfana da wannan shiri sun hada da Djibouti, Eritrea, Habasha, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan da kuma kasar Uganda.

Sanarwar ta ce, wannan shiri wata sabuwar dama ce da al'ummomin wadannan kasashe da ke kusurwar Afirka za su yi amfani da ita wajen samun ruwan sha mai tsafa, abinci mai gina jiki, kayayyakin kiwon lafiya, ilimi da kuma guraben ayyukan yi.

Bugu da kari, bankin duniya ya ba da sanarwar kara samar da tallafin kudi dala biliyan 1.8 don inganta ayyukan raya tattalin arziki, rage talauci da kuma bunkasa kananan sana'o'i a yankin.

Sai dai masu bayar da agajin sun bayyana cewa, duk da irin wadannan agaji da ake baiwa kasashen da ke wannan yanki, babbar matsalar da suke fuskanta ita ce ta cin hanci, fashin teku, fataucin makamai da miyagun kwayoyi da kuma ayyukan ta'addanci.

Sauran sun hada da rashin aikin yi tsakanin matasa, baya ga bambancin jinsi da mata ke fuskanta. A mako mai zuwa ne ake sa ran shugaban bankin duniya Jim Yong Kim zai ziyarci Nairobi, babban birnin kasar Kenya don tattauna yadda shirin zai amfani al'ummomin wadannan kasashe. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China