in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya ba da taimakon kudi dalar miliyan 160 ga Saliyo
2014-12-04 14:18:31 cri

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya bayyana cewar, bankin duniya ya baiwa kasar Saliyo taimakon kudi har dalar Amurka miliyan 160, a matsayin tallafi na yaki da cutar Ebola a kasar.

Shugaban bankin duniyar ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai jim kadan bayan ya tattauna da shugaban kasar ta Saliyo, Ernest Bai Koroma a gidan gwamnati.

Shugaban bankin ya kuma ce, bankin na ci gaba da nemawa kasar ta Saliyo guddumuwar kudade daga sauran kasashe na duniya.

Kim ya kuma yi alkawarin cewar, bankin na duniya zai ci gaba da tallafawa Saliyo gudanar da wani shiri da aka shirya, musamman a sakamakon farfadowar da Saliyon ta yi daga matsalar yaduwar cutar Ebola. Shirin wanda zai dau tsawon shekaru uku ana gudanar da shi, zai mai da hankali wajen samar da ababen jin dadi na rayuwa, musamman samar da lantarki da aikin noma.

A yayin da yake jawabi, shuagaban kasar ta Saliyo Bai Koroma ya godewa kasashen waje bisa kokarin da suke yi na taimakawa kasar ta Saliyo.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China