Bankin duniya ya ba da rancen kudi kashi biyu na darajar dalar Amurka miliyan 130 ga kasar Zambiya, kashin farko domin taimakawa 'yan matan da suka fito iyalai matalauta domin samun ilimi, kana kashi gudan domin kyautata ayyukan kiwon lafiya, in ji wata sanarwa a ranar Laraba.
Kwamitin zartaswa na bankin duniya ya amince ba da rancen dalar Amurka miliyan 65 domin shirin ilimantar da 'yan mata da samar wa mata 'yancin gudanar da harkokin tattalin arzikin na kashin kansu, da manufar taimakawa gwamnatin Zambiya kara hanyoyin taimakawa mata ta fuskar tattalin arziki, da samar da karatun sakandare ga 'yan matan da iyalansu ke fama da talauci.
Mahimman mutanen da gajiyar wannan shirin ta shafa su ne mata kimanin dubu 75 masu shekarun aifuwa daga 19 zuwa 64 dake da karfin yin aiki, da kuma 'yan mata kimanin dubu 14 masu shekarun aifuwa daga 14 zuwa 18 dake rayuwa cikin mawuyacin hali a yankunan karkara, in ji wannan sanarwa da reshen cibiyar bankin duniya a Zambiya ya fiyar.
Darektar bankin duniya reshen Zambiya, madam Kundhavi Kadiresan, ta bayyana cewa, bankin na fatan ganin ko da yaushe 'yan mata na kammala karatunsu na sakandare, kana kuma ana samun karin mata dake shiga cikin harkokin tattalin arziki, domin wadannan ne muhimman matakai na rage kaifin talauci a yankunan karkara.
Haka kuma bankin duniya ya kara ba da wani rancen kudi na dalar Amurka miliyan 65 domin kyautata ayyukan kiwon lafiya ga jama'a a birnin Lusaka, hedkwatar wannan kasa. (Maman Ada)