A jiya da yamma ne, bisa agogon Brussels, Li Keqiang, firaministan kasar Sin da Jean-Claude Juncker, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Turai wato EU suka halarci taron kolin masana'antu da kasuwanci na kasashen Sin da Turai, inda kuma ya yi wani jawabi.
Li Keqiang ya ce, a matsayinta na kungiyar kasashe masu sukuni mafi girma da kuma rukunin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, kungiyar EU na taka muhimmiyar rawa a al'amuran siyasa na kasa da kasa. Kasar Sin kuma kasa ce mai tasowa kuma mafi girma a duniya. A matsayinsu na manyan rukunoni 2 na kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, an dora musu nauyin hada kai wajen kara inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya ta fuskar karfin samar da kayayyaki.
A nasa bangaren, mista Juncker ya ce, kasar Sin na daya daga cikin muhimman abokan EU ta fuskar yin ciniki. Turai na kulawa sosai kan matakan da Sin ke dauka wajen aiwatar da manufofin raya tattalin arziki. Don haka tana son hada kai da Sin wajen inganta hadin gwiwarsu a fannonin cudanya da juna a sassa daban daban da kuma raya ababen more rayuwar jama'a. Har wa yau EU na yaba wa kokarin da kasar Sin ke yi wajen rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, don haka bangarorin 2 za su zurfafa hadin gwiwarsu a wannan fannin. (Tasallah Yuan)