in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Faraministan kasar Sin ya bar Beijing domin halartar dandalin shugabannin EU da Sin da kuma ziyartar Faransa
2015-06-28 14:27:35 cri
Faraministan kasar Sin Li Keqiang ya bar Beijing a ranar Lahadi da safe domin halartar dandalin shugabannin EU da Sin karo na 17 a birnin Brussels tare da kai ziyarar aiki a kasar Faransa, tare da rakiyar matarsa Cheng Hong.

A tsawon lakacin da zai kwashe a Brussels, mista Li zai jagoranci dandalin shugabannin EU da Sin tare da shugaban kungiyar tarayyar Turai Donald Tusk da kuma babban kwamishinan tarayyar Turai Jean-Claude Juncker. Haka kuma mista Li zai gana da faraministan kasar Belgium Charles Michel.

Bayan Brussels, Li Keqiang zai wuce zuwa kasar Faransa bisa goron gayyatar takwaransa na kasar Faransa Manuel Valls. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China