A lokacin tattaunawar Li Keqiang ya bayyana cewa, a matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin tana son hada kan sassa daban daban wajen tsara wani dawaumammen shirin na muradan karni bayan shekarar 2015 cikin hadin gwiwa kuma cikin adalci bisa shirin muradan karni da aka tsara a shekarar 2000 domin kokarin cimma burin kawar da talauci da neman bunkasuwa tare.
Haka kuma Li Keqiang ya nuna cewa, kasar Sin tana son amfana daga fasahohin da ta samu da kuma yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya domin kokarin samun dawaumammen ci gaba tare. Kasar Sin, in ji shi, da sauran kasashe masu tasowa da kasashe masu arziki su yi hadin gwiwa tsakanin bangarori biyu ko tsakanin bangarori uku, wanda zai zama wata muhimmiyar hanya ga matakin taimaka wa juna wajen neman farfado da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya gaba daya.
Bugu da kari, Firaministan na kasar Sin ya jaddada cewa, yanzu halin da kasar take ciki ta fuskar tattalin arziki yana da kyau. Don haka yana fatan masana za su ba da karin shawarwari da kuma gudummawar da ya kamata a kokarin fahimtar juna da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. (Sanusi Chen)