in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da wakilai mahalarta taron koli na kwamitin jami'an CEO na duniya
2015-06-10 11:34:03 cri

Da yammacin jiya Talata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da wakilai mahalarta taron koli na tattaunawa, karo na 3 na kwamitin manyan jami'an zartaswa CEO na duniya, taron da ya gudana a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.

Mr. Li ya zanta da wasu daga wakilan manyan kamfanoni da suka hada da na kamfanin BHP Billiton Ltd, da na Honeywell, da Das AutoVolkswagen, da Nokia, da Pfizer Pharmaceuticals, da Goldman Sachs da dai sauransu. Ya kuma yi musayar ra'ayoyi da su game da babban taken taron, wato "Hanyar da kasar Sin za ta bi wajen samun cikakken karfin takara bisa sabon tsarin duniya".

Kaza lika sun tattauna kan batutuwan da suka shafi yanayin da Sin ke ciki a fannin zuba jari, da manufofin da kasar ke gudanarwa game da fannin, inda firaminista Li ya yi tsokaci game da tambayoyi da aka gabatar.

Mr. Li ya bayyana cewa, a halin yanzu tattalin arzikin duniya na fuskantar matsaloli wajen farfadowa, kuma kasar Sin ma na fuskantar irin na ta matsala ciki hadda raguwar saurin bunkasar tattalin arziki. Don haka ya ce akwai bukatar samar da sabon karfi, idan har ana da burin tabbatar da samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata.

Ya ce ayyukan da ake gudanarwa yanzu, na karawa jama'a kwarin gwiwa wajen kafa kamfanoni, da kirkire-kirkire, da daukar muhimmin muhimman matakan gyare-gyare, dukka dai da nufin cimma nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci, da karafafa ikon kasa, da samar da moriya ga jama'ar ta.

Bugu da kari, firaministan ya jaddada da cewa a yanayin da ake ciki na bunkasuwar tattalin arzikin duniya bai daya, da gudanar da cinikayya cikin 'yanci ke bayarwa a duniya, ana dada zurfafa hadin kai tsakanin sassan tattalin arzikin Sin da na duniya, kana kasar ta Sin tana ta kara bude kofa a sabon zagaye ga kasashen ketare.

Har wa yau a cewar sa gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai a fannonin ba da iznin sayar da kayayyaki, da ba da hidima a fannin kudi, da kiyaye ikon mallakar fasaha, da dai sauransu, ta yadda za ta daidaita kau da bambancin da aka nuna ma kamfanonin Sin da na kasashen ketare zuwa matsayi guda, domin kafa wata kasuwa mai adalci. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China