Yau Jumma'a 29 ga wata, firaministan Sin Li Keqiang ya isa birnin Beijing, bayan da ya kammala ziyarar da ya kai a kasashen Brazil, Columbiya, Peru da Chile a hukunce, inda ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, wanda ya rufa masa baya a wannan ziyara ya shaidawa wakilinmu cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu.
Wang Yi ya ce, muhimmin sakamakon da aka samu a wannan ziyara shi ne, bangarorin biyu sun yi amfani da hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannin masana'antu, wajen kafa nagartattun masana'antu da fitar da nau'rorin zamani zuwa kasashen dake yankin kudancin Amurka, don raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, tare da karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu.
Minista Wang ya kara da cewa, ziyarar firaministan Sin a kudancin Amurka ta bude sabon shafin raya makomar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashe masu tasowa, inda firaministan ya gabatar da shawarwarin raya hadin gwiwa a fannoni 3 wato kafa hanyoyin sufuri, wutar lantarki, da harkokin sadarwa, da sa kaimi ga masana'antu da zamantakewar al'umma, da gwamnatocin kasashen biyu su shiga ciki, kana da yin amfani da asusun ba da lamuni, da ba da rance, da kudin inshora don gudanar da su, kuma wannan shawara ta samu karbuwa daga kasashen da ke yankin kudancin Amurka, saboda makoma ce mai haske wajen raya hadin gwiwar bangarorin biyu.(Bako)