Uwar gidan firaministan Sin Cheng Hong, da shugabar kasar Chile Michelle Bachelet, da babbar sakatariyar zartaswar hukumar ECLAC Alicia Barcena, na cikin wadanda suka samu halartar taron.
Firaministan Li ya ce, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake yankin kudancin Amurka ta shiga wani sabon mataki na hadin gwiwa daga dukkanin fannoni.
Li Keqiang ya ce, Sin babbar kasa ce dake cikin gamayyar tattalin arzikin duniya. Ya kuma yi imanin cewa za a raya tattalin arzikin yadda ya kamata. Kuma a nan gaba za a dauki wasu karin matakai na sa kaimi ga raya tattalin arziki cikin sauri ko matsakaicin sauri. Har wa yau Sin za ta karfafa manufar bude kofa ga kasashen waje a sabon zagaye, don samar da babbar damar samun ci gaba ga kasashe daban daban.
Mambobin hukumar ECLAC da jami'an diplomasiyyar kasashen duniya da ke Chile kimanin 300, sun nuna maraba da jawabin na firaministan kasar Sin. (Bako)