Asusun na IMF ya kuma gabatar da wani rahoto game da kungiyar G20 a wannan rana, inda ya ce, bayan da aka gabatar da rahoton hasashen da ake kan tattalin arzikin duniya a farkon watan Oktoba, an samu ci gaba a tattalin arzikin duniya, ciki har da kyautata kasuwar hada-hadar kudi, raguwar farashin mai, yayin da aka samu sassaucin bunkasuwar tattalin arziki a wasu kasashe masu ci gaba.
Rahoton ya yi nuni da cewa, yanayin hada-hadar kudi a yanzu yana iya taimakawa kasashen duniya wajen farfado da tattalin arzikinsu, amma kwan gaba kwan baya a kasuwar hada-hadar kudi da aka samu a kwanakin baya ya nuna hadarin raguwar tattalin arzikin da za a fuskanta a nan gaba.
Hasashen da rahoton ya gabatar ya yi daidai da rahoton hasashen da aka yi kan tattalin arzikin duniya da aka gabatar a watan Oktoba, inda aka zaci cewa, a shekarar 2014 tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 3.3 cikin dari, kuma saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya a badi zai karu zuwa 3.8 cikin dari. (Zainab)