Da take Magana a Jami'ar Georgetown a lokacin taron shekara shekara na hadin gwiwwa tsakanin bankin duniya da asusun, Madan Madam Lagarde tace tattalin arzikin duniya bashi da karfi fiye da yadda ake tsammani kuma zai karu dan kadan ne a shekara mai kamawa domin hasashen da ake na farfadowar sa ya kara ja da baya.
Ta ce shekaru 6 tun da aka fuskanci rikicin tattalin arziki na duniya baki daya har yanzu ana cigaba da fuskantar koma baya a wannan bangaren.
Shugabar asusun daga nan sai tayi nuni da cewar har yanzu akwai yanayin dake nuna cewa ba'a fita daga rikicin tattalin arzikin duniya ba kuma wassu kasashe da a da hakan bai shafe su kwarai ba ma yanzu akwai yuwuwar yiwuwar zai shafe su don haka tayi kira ga hukumar ajiyar kudi data yi kokarin isar da sako ga kasuwanni game da ficewar sassaucin da kasuwannin suke samu a da.
Ta kuma yi hasashe game da cigaba da karuwar zaman dar dar a yankuna abin da zai kawo barazana ga ci gaban tattalin arzikin duniya, sannan hakan zai tsananta yanayin da ake ciki a kasar Ukraine ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi,kasuwannin hannun jari da ciniki. Barkewar cutar Ebola a Afrika shi ma zai iya kawo babbar barazana a Jacquesyankin dama duniya baki daya idan har ba'a shawo kansa yadda ya kamata ba. (Fatimah)