IMF ya ce yana da nufin samar da gudummawar kudi, ga kasashe masu fama da talauci dake fuskantar manyan bala'u, ko cututtuka, da rage basussukan da ake bin su, a wani mataki na taimakawa kasashen ta yadda za su samu damar amfani da albarkatunsu wajen yaki da bala'i, da kuma sake gina kasa bayan aukuwar hakan.
Majalisar IMF ta tsaida kudurin cewa, asusun samar da taimakon zai soke basussuka kimanin dala miliyan 100 da ake bin kasashen Liberia, da Saliyo da Guinea, bisa kudurin na tallafa musu biya basussuka.
Bugu da kari, majalisar IMF tana da shirin samar da rancen-gata da ya kai dala miliyan 160 ga wadannan kasashe uku. (Zainab)