A halin yanzu wakilin sashen Hausa na gidan rediyon CRI dake Najeriya Murtala Zhang yana wata ziyara a birnin Kano. Kuma a yau, ya ziyarci gidan rediyon Freedom, inda ya bayyana ra'ayinsa game da birnin Kano da al'ummarsa.
Haka kuma Murtala ya gana da wasu tsofaffin masu sauraron sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin, ciki har da Malam Garba Baji da Malam Yahaya Amadu dan Arewa.
Allah ya bar zumunci. Amin!