Haka kuma, kwamitin tsaron MDD ya kuma fidda wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, domin yin suka kan lamarin, inda ya kuma jaddada cewa, ya kamata a gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi gaban kuliya.
Kaza lika, shugaban babban taron MDD Sam Kahaba Kutesa ya ce, hare-haren ta'addanci da aka aiwatar a wannan rana sun sake nuna cewa, gamayyar kasa da kasa ba za su yi hakuri ko kadan kan tashe-tashen hankula na masu tsattsauran ra'ayi ba, ya kamata su dukufa wajen shiga ayyukan yaki da ta'addanci.
A wannan rana ta Jumma'a 26 ga wata, wasu dakaru suka kai hari ga wani otel dake birnin Sousse na kasar Tunisia, harin da ya haddasa rasuwar mutane 37, yayin da 36 suka jikkata, kana an kuma kai harin boma-bomai ga wani masallacin dake babban birnin kasar Kuwait, Al Kuwayt, inda aka halaka mutane 27, yayin da 222 suka jikkata. A wannan rana kuma har ila yau, an kai hari ga wani masana'anta a lardin Isere dake gabashin kasar Faransa, wanda ya halaka mutum daya, yayin da wasu suka jikkata. (Maryam)