in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya isa kasar Chile
2015-05-25 10:39:49 cri

Bisa gayyatar da shugaban kasar Chile Michelle Bachelet ya yi masa, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Saint Diego a jiya Lahadi tare da mai dakinsa Cheng Hong, domin fara ziyarar aiki a kasar ta Chile.

Da yake jawabi jim kadan da saukarsa, Mr. Li ya bayyana cewa kasar Chile ita ce kasa ta farko da ta kulla dangantakar diplomasiyya da kasar Sin a nahiyar kudancin Latin Amurka, kana ita ce kasa ta farko da ta daddale yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tare da kasar Sin a latin Latin Amurka.

Ya ce wannan ziyara ta sa, na da nufin zurfafa zumunci dake tsakanin kasashen biyu, da kara fadada amincewa da juna a fannin siyasa, da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin raya yankin ciniki cikin 'yanci, na Sin da Chile, da bunkasa hada-hadar kudi, da samar da kayayyaki, da gina ababen more rayuwa da dai sauransu.

Ana dai s a ran yayin wannan ziyara, Li Keqiang zai gana da shugaba Bachelet, kuma za kuma su gudanar da taron 'yan jarida na hadin gwiwa. Zai kuma halarci taron tattaunawa game da tattalin arziki, da cinikayya, a gabar da ake cika shekaru 45 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Chile, da kuma taro na 7 na kwamitin 'yan kasuwar kasashen biyu.

Haka zalika kuma, Li Keqiang zai yi jawabi ga kwamitin tattalin arziki na na MDD na Latin Amurka da tekun Caribbean. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China