in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya halarci jerin ayyukan karawa juna sani a fannin al'adu tsakanin Sin da Latin Amurka
2015-05-24 17:00:23 cri

A safiyar jiya Asabar 23 ga watan nan ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya kai ziyara a dakin adana kayayyakin tarihi, da na bunkasa ilimin bil'adam, da bincike ga kayayyakin tarihi dake birnin Lima, hedkwatar kasar Peru, inda ya halarci jerin ayyukan karawa juna sani a fannin al'adun kasashen Sin da na Latin Amurka.

Li ya ce, Sin da Peru na matukar girmamawa al'adun juna, hakan ne kuma ya sa bangarorin biyu ke fatan koyon darussa daga juna. Kaza lika ana fatan hakan zai taimaka wajen zurfafa mu'amala a fannin al'adu tsakanin kasashen biyu cikin kuzari.

Har wa yau Mr. Li ya bayyana fatan kasashen biyu za su cimma sabbin nasarori da sakamako mai kyau bisa hakan. Dadin dadawa, Li ya yi fatan alheri ga al'ummar kasar ta Peru.

A nasa bangare, shugaban majalissar ministocin Peru Pedro Cateriano Bellido, ya bayyana cewa duk da nisan dake tsakanin Peru da Sin, a hannu guda dankon zumuncin dake tsakanin kasashen na da matukar inganci. Ya ce tun da can, akwai Sinawa da dama da suka yi kaura zuwa Peru, inda suke shiga ayyukan raya kasa, da na zamantakewa tare da jama'ar Peru yadda ya kamata.

Bugu da kari Mr. Bellido ya ce Sin da Peru aminan juna ne, kuma ba za a iya sanya wani shinge a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da sauran fannoni tsakaninsu ba. Har wa yau Peru na fatan karfafa dangantaka tsakaninta da kasar Sin, a kokarinta na bude sabon babi tare da kasar ta Sin. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China