Kasar Sin ta bayyana farin cikinta game da yadda gwamnatin kasar Mali ta daddale yarjejeniyar zaman lafiya da wasu kungiyoyin dakaru
Dangane da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya da wasu kungiyoyin 'yan tawaye dake arewacin Mali suka daddale tare da gwamnatin kasar ta Mali, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, Hong Lei ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin ta yi maraba da ganin cewa, an sami babban ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Mali.
Hong Lei ya ce, Sin ta na kira ga bangarorin daban daban na Mali da su yi amfani da wannan zarafi, su sa kaimi ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya zuwa wani sabon mataki, a kokarin cimma burin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin dogon lokaci.
A ranar jumma'ar makon jiya ne dai gwamnatin kasar Malin ta rattaba hannu kan yarjejeniyar da wassu kungiyoyin 'yan tawaye.(Fatima)