Zaunanen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a gun taron muhawara da MDD ta yi kan batun yaran da tashin hankalin da ke yi da makamai a jiya Alhamis cewa, daidaita rikici da tsagaita bude wuta su ne hanyoyin da suka dace wajen kare rayukan yara yayin rikici.
Liu Jieyi ya ce, hakkin kwamitin sulhu na MDD ne ya kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya, don haka kamata ya yi a mayar da hankali ga daukar matakan diflomasiya don rigakafin rikici ta hanyoyin shiga tsakani da yin shawarwari da musayar ra'ayi kamar yadda tsarin dokar MDD ya kayyade, kana kamata ya yi a karfawa bangarori daban daban da rikicin ya shafa da su daidaita sabannin da ke tsakaninsu ta hanyar lumana, domin fitar da yara daga tashe-tashen hankula.
Ban da haka kuma, Liu Jieyi ya ce, hakkin gwamnatin da ta rikici ne ta kare rayukan raya. Kamata ya yi kasashen duniya su taimaka tare da ba da goyon baya ga gwamnatin kasar tare da martaba 'yancita domin kara karfinta na kare rayukan yara.
Bugu da kari, Liu Jieyi ya ce, kasar Sin a shirye ta ke ta yi aiki kafada da kafada da kasashen duniya wajen samar da zaman lafiya da tsaro a duniya, domin kyautata rayuwar yaran dake fama da rikici, ta yadda za a samar da yanayin da ya dace ga rayuwar wadannan yara.(Lami)