in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allawadai da kisan mutane 9 a Caroline ta Kudu dake Amurka
2015-06-19 10:51:32 cri

Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya yi allawadai da babbar murya a ranar Alhamis game da kisa mutane tara a yayin wani taron addu'a a cikin wata tsofuwar majama'a ta bakaken fata dake tsakiyar birnin Charleston, a jihar Caroline ta Kudu, dake kudu maso gabashin kasar Amurka.

Sakatare janar ya yi allawadai da wannan barin wuta, wanda daga dukkan alamu na da nasaba da wariyar launin fata, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara a cikin wannan majama'a da 'yan Amurka bakaken fata na birnin Charleston ke yawan zuwa a ranar 17 ga watan Juni, in ji mataimakin kakakin MDD Farhan Haq a yayin wani taron manema labarai na mako mako a cibiyar MDD dake birnin New York.

Mista Ban na aika ta'aziyarsa ga iyalan mamatan, tare da fatan murmurewa ga wadanda suka tsirar da rayukansu, in ji mista Haq. Kuma yana fatan ganin mutanen dake da hannu kan wannan lamarin nuna kiyayya da tashin hankali, a gurfanar da su gaban kotu.

An cafke wani mutum dauke da bindiga da ake zargi da kashe wadannan mutane tara a ranar Alhamis da safe a birnin Shelby dake jihar Caroline ta Arewa, a cewar 'yan sandan wurin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China