in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kasance wuri na biyu da kasashen waje suka zuba jari a duniya
2015-06-18 11:20:02 cri
A kwanakin baya ne hukumar da ke nazarin harkokin kasuwancin kasa da kasa ta Ernst &Young ta gabatar da wani rahoton bincike kan karfin nahiyar Airka na jawo hankalin masu zuba jari, inda aka bayyana cewa, yawan jarin da kasashen waje suka zuba jari kai tsaye a nahiyar Afirka a shekarar 2014 ya karu da kashi 136 cikin dari bisa na shekarar 2013, adadin da ya kai dala biliyan 128.

Don haka, nahiyar Afirka ta kasance wuri na biyu da kasashen waje suka zuba jari a duniya, yayin da nahiyar Asiya ta zama na farko.

Rahoton ya bayyana cewa, an samun karuwar jarin da aka zuba kai tsaye a nahiyar Afirka a shekarar 2014 a sakamakon yadda aka gudanar da ayyukan fadada mashigin kogin Suez a kasar Masar. Kuma wannan ya taimaka wajen kara samar da ayyukan yi kimanin dubu188 ga nahiyar Afirka.

Rahoton ya kara da cewa, kasashen da suka zuba jari ga nahiyar Afirka kai tsaye sun hada da Amurka, Britaniya, Faransa, hadaddiyar daular Larabawa, Portugal, Jamus, Sin, Indiya da dai sauransu, wadanda suka fi mai da hankali kan zuba jari a fannonin ayyukan more rayuwa, makamashi, rukunin gidaje, wuraren cin abinci, kafofin watsa labaru, sadarwa, hidimar hada-hadar kudi, fasahohin kere-kere na zamani da dai sauransu.

Wannan ne shekara ta biyar a jere da hukumar Ernst &Youn ta gabatar da rahoton bincike kan karfin jawo hankali na nahiyar Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China