Wani kamfanin tuntuba game da harkokin zuba jari mai suna "C-NERGY Global Holdings", ya shirya jagorantar babban taron tattaunawa kan hanyoyin da za a bi, wajen bunkasa harkokin hadin gwiwa a fannin zuba jari a kasar Ghana.
Ana dai fatan gudanar wannan taro na karawa juna sani, wanda kamfanin na C-NERGY, da hadin gwiwar ma'aikatar kudi da zuba jarin kasar za su dauki nauyin shiryawa cikin watan Agusta mai zuwa.
Taken taron dai shi ne "shawo kan gibin ababen more rayuwa a Ghana".
Da yake karin haske game da muhimmancin taron, daraktan kamfanin na C-NERGY George Fosu, cewa ya yi, tattaunawar za ta share fagen aiwatar da tsare-tsare masu ma'ana, a fannonin hadin gwiwar zuba jari, karkashin kudurori, da dokoki da tuni aka tsara domin cimma nasarar hakan.
Ita ma a nata bangare, daraktar sashen zuba jari a fannonin da ba na gwamnati ba, ta ma'aikatar kudi da zuba jarin kasar ta Ghana Magdalene Ewurasi Apenteng, cewa ta yi, gwamnatin kasar na fuskantar kalulabe na babban gibi a fannin samar da ababen more rayuwa, don haka akwai bukatar karfafa shigar sassa masu zaman kan su domin cike gibin dake akwai. (Saminu)