Kamfanin binciken harkokin kudi na Ernst&Young ya fitar da wani rahoto game da karfin kasashen Afrika a fannin jawo jarin da aka zuba musu a shekarar 2015, inda aka bayyana cewa, yawan kudaden da kasar Sin ta zuba wa kasashen Afrika a shekarar 2014 ya karu zuwa dalar Amurka biliyan 6.1 wato kimanin kashi 166.7 cikin dari, wadanda suka shafi ayyuka 32, hakan ya sa kasar Sin ta sha gaban kasar India wajen zama ta 7 ta fuskar zuba jari a Afrika, kuma kasashe 6 dake kan gaba su ne kasashen Amurka da Birtaniya da Afrika ta kudu da Saudiyya da Faransa da kuma Jamus.
Rahoton ya ce, manyan ayyuka 3 da kasar Sin ta fi zuba jari a kansu su ne ayyukan sadarwa da watsa labaru da kuma kimiyya da fasaha (TMT), wadanda suka dauki kashi 1 cikin 3 na daukacin jarin da ta zuba. Kana kasar Afrika ta kudu ta fi yawan ayyukan da kasar Sin ta zuba musu jari, wadda ta samu kashi 34.4 cikin dari na daukacin ayyukan da kasar ta Sin ta zuba jari a kai, kasashen dake biye da ita su ne kasashen Tanzaniya da Ghana da kuma Kenya.(Lami)