Masana'antar harkokin kudin kasa da kasa (SFI) ta hukumar bankin duniya ta yi shirin zuba jarin a kalla dalar Amurka biliyan biyu a kowace shekara a bangaren noma a nahiyar Afrika har zuwa nan da shekarar 2018. Shugaban SFI, reshen kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara, German Vegarra ya bayyana a ranar Alhamis a yayin wani taron manema labarai a Nairobi cewa, a tsawon shekarar da ta gabata game harkokin kudi a fannin noma, jimillar jarin da aka zuba a wannan shiyya ta kai dalar Amurka biliyan daya. Zuba jari a fannin noma wata dabara ce ta SFI, ganin yadda kalubalolin tsaron abinci da suke karuwa a nahiyar Afrika, in ji mista Vegarra. (Maman Ada)