Mahalarta dandalin bunkasa cigaban Afrika (ADF-IX) karo na tara, sun yi kira a ranar Talata a birnin Marrakech, da a kafa wani tsarin doka da ya dace domin bunkasa zuba jari a Afrika, a cewar kamfanin dillancin labarai na MAP.
Masu gabatar da jawabai a lokacin zaman taron da aka gudanar bisa taken "Yanayin jarin masu zaman kansu a Afrika da karfinsa a matsayin wata hanyar zuba jari, taimakawa cigaba da kuma samar da guraben aikin yi", sun nuna cewa, gwamnatocin Afrika, suna da babban matsayin da ya rataya kansu wajen bunkasa tsarin zuba jari, dake kasancewa wani muhimmin karfin zuba jari a fannin samun bunkasuwa da cigaba. A cewar darekta kuma wanda ya kafa kungiyar Emerging Markets Private Equity Association (EMPEA), Mike Casey, zuba jari zai iyar taimaka ga gaggauta cigaban Afrika a lokaci guda da sauran nahiyoyi.
Sakataren kasa kan cigaba da kuma dangantakar kasa da kasa na kasar Tunisia, Noureddine Zekri, ya nuna cewa, kasarsa ta cimma wani tsarin doka da ya taimaka karara wajen kara yawan kamfanoni matsakaita da kuma kanana. (Maman Ada)