in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuba jari a noma da gine-gine za su taimaka wa cigaban Afrika
2014-10-08 10:34:21 cri

Zuba jari yadda ya kamata a fannonin noma, gine-gine, cibiyoyin hada-hadar kudi da sadarwa za su iya taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin Afrika, in ji bankin duniya a ranar Talata.

A cikin wani rahotonsa na baya bayan nan kan nahiyar Afrika, bankin duniya ya bayyana cewa, kyautatuwar mizalin bunkasuwa zai iyar farfadowa a cikin wani yanayin faduwar farashin kayayyakin bukatun farko da raguwar zuba jarin waje na kai tsaye dalilin matsalar tattalin arzikin duniya.

Farashin kayayyakin bukatun farko na kasancewa muhimmin abu ga makomar Afrika domin wadannan albarkatu na cigaba da wakiltar kashi uku bisa hudu na jimillar kayayyakin da kasashen dake kudu da hamadar Sahara suka fita zuwa kasashen waje, in ji Pulse, wani binciken dake fitowa a duk watanni shida da bankin ya gudanar kan batutuwan dake shata makomar tattalin arzikin Afrika.

Duk da cewa bunkasuwar tattalin arzikin duniya na kasa da hasashen da aka yi, amma tattalin arzikin nahiyar zai cigaba da karuwa sannu a hankali, tare da hasashen bunkasuwar GDP na shiyyar da kashi 5,2 cikin 100 a kowace shekarar a shekarar 2015 da ta 2016, kana da kashi 4,6 cikin 100 a shekarar 2014.

Bisa hasashen, a dunkule, tattalin arzikin yankuna uku a Afrika zai samu cigaba cikin sauri, kuma zai cigaba da karuwa ba tare da tsaya ba tun yau da shekaru ishirin, in ji Francisco Ferreira, masanin tattalin arzikin na bankin duniya reshen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China