Mr. Graaff ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, ko da yake an samu nasara sosai wajen tinkarar cutar Ebola, amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba. Sannan ya nuna cewa, yanzu za a shiga lokacin damina a yankin yammacin Afirka, sakamakon haka, za a kara fuskantar sarkiya da wasu wahalhalu wajen shawo kan cutar ta Ebola. Har ma yanzu ana kusan rasa damar shawo kan cutar. Sabili da haka, kada saurin yaduwar annobar ya wuce kokarin da ake na shawo kan cutar."
Bugu da kari, Mr. Graaff ya nuna cewa, kafin a samu nasarar shawo kan cutar a dukkan kasashen da cutar ta shafa gaba daya, cutar Ebola na iya zama wata barazana mai tsanani ga yankin yammacin Afirka, har ma duk duniya. Don haka ya zama wabiji a mai da hankali a cikin makonni masu zuwa, kan dukkan wadanda suka kamu da cutar. (Sanusi Chen)