Hakan a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Laberiya, ya biyo bayan ayyana kasar da hukumar Lafiya ta duniya WHO ta yi, da cewa ta fita daga kangin Ebola.
Tuni dai 'yan kasar, da sauran abokan arziki suka bayyana matukar farin ciki da jin wannan albishir, musamman duba da yadda a baya Laberiyan ta kasance cikin kasashen yammacin Afirka uku, da wannan cuta tafi kamari.
Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran isar shugabanni da dama kasar ta Laberiya, ciki hadda shugaban kasar Togo, kuma wakilin kungiyar ECOWAS a yaki da cutar Ebola Faure Gnassingbe, da shugaban hukumar kungiyar Kadre Desire Ouedraogo. Sauran baki da ake fatan za su halarci bikin sun hada da ministar harkokin wajen kasar Ghana Hanna Tetteh, da ministan lafiyar tarayyar Najeriya Dr. Khaliru Alhassan, da kuma sauran wakilai daga sassan duniya da dama. (Saminu Hassan)