in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Banbancin manufar siyasa na cikin manyan dalilai da suka kawo tsaiko a yaki da Ebola
2015-05-07 10:52:59 cri

Wakilai daga kasashen Guinea, da Liberia da Saliyo, sun shaidawa kwamitin bincike da MDD ta kafa cewa, banbancin ra'ayi a siyasance tsakanin kasashen da suka sha fama da cutar Ebola, na cikin manyan dalilan da suka haifar da tsaiko ga yaki da cutar.

Hakan dai na kunshe ne cikin wani rahoto da aka fitar a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya. Cikin rahoton, wakilan kasashen uku sun ce, matsalar talauci, da koma baya a fannin kiwon kafiya, su ma sun taimaka wajen rage tasirin yaki da cutar.

Wakilan sun gabatar da tsokacin ne a birnin New York, yayin zaman kwamitin da MDD ta kafa, domin bincikar halin da ake ciki game da daukar matakan dakile matsalolin lafiya a duniya, karkashin jagorancin shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete.

Da yake tsokaci game da hakan, jakadan kasar Guinea a MDDr Mamadi Toure, ya ce, duk da gano bullar cutar ta Ebola da aka yi cikin hanzari, ba a iya kaiwa ga dakile ta ba, duba da yadda al'ummun kasashen suka rika nuna halin ko-in-kula, da kuma banbance-banbance a manufofin siyasa, tsakanin kasashen da batun ya shafa.

Dukkanin wakilan kasashen uku dai sun yi amannar cewa, da farko-farkon bullar cutar Ebola, al'ummar kasashen sun kadu matuka, ta yadda ba a iya daukar wasu managartan matakai da suka dace ba.

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ne ya kafa kwamitin mai mambobi daga kasashen Brazil, da Amurka, da Botswana, da Indonesia da kuma Switzerland, domin zakulo hanyoyin tunkarar annoba a nan gaba. Ana kuma sa ran Mr. Ban zai gabatar da sakamakon binciken gaban zauren MDD, domin daukar sauran matakan da suka dace. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China