in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya
2015-06-17 21:10:38 cri

Da yammacin yau Laraba 17 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya ko (WEF) Mr. Klaus Schwab a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu Mr. Li ya bayyana cewa, a halin da ake ciki, ana ci gaba da gudanar da kwaskwarima ga tattalin arzikin duniya, kana tattalin arziki na farfadowa duk da matsalolin da ake fuskanta.

Ya ce a daidai wannan lokaci kuma, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya ragu. Don haka kasar ta Sin ke aiwatar da kwaskwarima a fannoni da dama, ciki hadda na saukaka hanyoyin gudanar da harkokin gwamnati, da kyautata hidimomin da ake bayarwa da dai sauransu. Kaza lika an karfafa aikin kulawa a wasu fannoni, da sa kaimi ga jama'ar kasar, wajen gudanar da harkokin kashin-kai, da sa kaimi ga bunkasa karfin kasuwanni, a kokarin samun karin ci gaban tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

Ban da haka, Li ya kara da cewa, za a gudanar da dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na Davos a watan Satumban bana. Kuma Sin na fatan kokari tare da WEF, wajen tabbatar da taken taron cikin hangen nesa, a kokarin samar da sabbin kayayyaki.

A nasa bangare, Mr. Schwab, cewa ya yi a farkon shekarar nan ta bana, firaminista Li ya gabatar da jawabi mai muhimmanci, yayin taron shekara-shekara na WEF na bana, wanda zai ba da gudummawa wajen kara kwarin gwiwa ga kasashen duniya a fagen samun karin ci gaban kasar Sin a nan gaba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China