Wakilan kasashe mambobin kungiyar tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin neman 'yanci ta fuskar kudi ga kungiyar. Suna son ganin kungiyar AU ta tsaya da kafafunta wajen samar da kasafin kudin gudanar da aikinta na shekarar 2016, in ji shugaban kwamitin zartaswa na AU, Simbarashe Mumbengegwi.
Kungiyar AU ta dauki niyyar zuba kundinta na gudanar da aiki ta hanyar amfani musammun ma da albarkatun cikin gida, in ji mista Mumbengegwi a gaban 'yan jarida a Johannesburg, inda taron kungiyar AU karo na 25 ke gudanarwa.
Daga bakin shekarar 2016, kasashe mambobin za su zuba kudi da kashi 100 bisa 100 na kudaden gudanar da aiki, a kalla kashi 75 cikin 100 na kasafin tsare tsare, da kuma a kalla kashi 25 cikin 100 na kasafinta domin ayyukan wanzar da zaman lafiya, in ji wannan jami'i.
Niyyar ta kasance wani muhimmin mataki da kungiyar ta dauka domin baiwa Afrika damar sanya ido ga tsare tsarenta da ayyukanta, in ji mista Mumbengegwi.
Haka kuma ya jaddada cewa, dole AU ta rayu gwargwadon kasafin kundita domin kaucewa ko da yau neman taimako daga abokan huldarta. (Maman Ada)