in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na duba yiwuwar bullo da tsarin kudi na bai daya a nahiyar
2015-06-12 10:03:10 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) na duba yiwuwar bullo da tsarin takardar kudi ta bai daya a wani bangare na ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063 da kungiyar ta tsara.

Kwamishinan kungiyar mai kula da harkokin tattalin arziki Anthony Mothae Maruping wanda ya bayyana hakan yayin taron kolin kungiyar karo na 25 da ke gudana a birnin Johanneburg na Afirka ta Kudu ya ce, manufar shirin ita ce hade nahiyar da kayayyakin more rayuwa na zamani da kaddamar da manyan ayyuka.

Bugu da kari, tsarin zai saukaka harkokin saye da sayarwa tsakanin kasashen da ke nahiyar wanda ake fatan gwada shi a kasashen da ke amfani da kudin Rand na Afirka ta Kudu karkashin tsarin kudi na bai daya.

Tuni dai gwamnonin manyan bankunan kasashen Afirka suka tattauna kan kafa asusun ba da lamuni na nahiyar, wanda shi ne sakamakon karshe game da shirin kungiyar na raya nahiyar nan da shekarar 2063.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China