in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta alkawarta shirya babban taron AU cikin nasara
2015-06-09 10:01:02 cri

Mahukuntan Afirka ta Kudu, sun alkawarta cimma nasarar babban taron kungiyar AU karo na 25 wanda kasar za ta karbi bakunci.

A cewar minista mai lura da ma'aikatar huldar kasashen waje Maite Nkoana-Mashabane, kasarta na fatan taron na bana mai lakabin "shekarar raya al'amuran mata da samar da ci gaba ga Afirka nan da shekarar 2063", zai samu halartar daukacin shugabannin nahiyar, da kuma wakilai da dama.

Mashabane ta kara da cewa, taron na bana zai mai da hankali ga nazartar irin ci gaban da aka samu a fannonin wanzar da zaman lafiya, da bunkasar zamantakewar al'ummar Afirka, tare da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen nahiyar, da kuma sauran masu ruwa da tsaki game da yaki da cututtuka, da kuma inganta kiwon lafiya.

Sauran sassan sun hada da yaki da talauci ta hanyar sauya dabarun bunkasa tattalin arziki, da kuma batun dunkule tattalin arzikin nahiyar ta hanyar samar da karin ababen more rayuwa. Ta ce, batun gyaran fuska game da ayyukan MDD na cikin abubuwan da za a tattauna, a fannin alakar AU da hukumomin kasa da kasa.

Kaza lika ministar ta ce, taron na AU zai binciko hanyoyin da za su dace kasashe mambobinta su bi, wajen daukar nauyin shirye-shiryensu, duk kuwa da karancin kudaden gudanarwa da ake fuskanta. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China