in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nemi shugabannin Afrika da su dakatar da rikicin 'yan ci rani
2015-06-12 10:58:23 cri

Shugabar kwamitin tarayyar Afrika (AU), Nkosazama Dlamini-Zuma ta yi kira a ranar Alhamis ga shugabannin Afrika da su yi iyakacin kokarinsu domin dakatar da rikicin 'yan ci rani a lokacin da matsalar 'yan ci ranin Afrika da ke kwarara zuwa nahiyar Turai ke kasancewa a sahun gaban jaridun kasa da kasa.

Rashin karfinmu na yin aiki zai iyar hadasa asara ga ci gaban da nahiyar ta samu a tsawon shekarun baya, in ji madam Dlamini-Zuma a yayin taron kungiyar AU karo na 25 da ke gudana a birnin Johannesburg.

Ta nuna cewa, akwai kalubaloli da kasashen Afrika za su iyar fuskanta na rashin kwararru, kuma tattalin arzikin da ke cikin mawuyacin hali za su iyar kara wahala, dalilin yawan 'yan ci rani da kuma masu neman aiki ke kokarin ficewa daga Afrika.

Yan Afrika dole su fitar da Afrika a lokacin da suke so, amma ba wai sai lokaci ya tilsata musu ba, in ji madam Dlamini-Zuma.

Idan 'yan Afrika suka ci gaba da barin nahiyar daki daki, nahiyar za ta fuskanci matsaloli domin cimma burin maradun ajandarta na shekarar 2063 na wata nahiyar da ke samun ci gaba cikin zaman lafiya da kanta, in ji madam Dlamini-Zuma a yayin bude taron kwamitin zartaswa na kungiyar AU, wani dandalin ministocin harkokin wajen wakilan kasashe mambobi 54 na kungiyar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China