in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ce ya kamata taron AU ya mai da hankali kan talauci da tsaro
2015-06-10 12:52:57 cri

An ba da shawara cewa, taron kungiyar AU da yanzu haka yake gudana a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu ya kamata ya mai da hankali ne a kan samar da hanyoyin da za'a yaye talauci a nahiyar, da kuma tabbatar da tsaro.

Wannan taro dai da aka fara a ranar Lahadi a Pretoria kafin a koma Johannesburg, na sa ran a kammla shi da taro tare da shugabannin gwamnatoci da kasashe a ranar 14 zuwa 15 ga watan nan na Yuni.

A cikin hirar da ya yi da Xinhua, Gideon Chitanga, wani mai bincike a cibiyar karatun harkokin demokradiya a jami'ar Johannesburg ya ce, taron yana ba da babbar dama ga shugabannin Afrika na tattauna hanyoyin magance talauci, wanda a cewar sa ya kai wani matsayi mai ban tsoro a nahiyar.

Ya ce, a yammacin Afrika, rashin aikin yi da kuma karuwar kangin talauci yana tilasta wa dubban matasa sadaukar da rayuwansu wajen tsallake tekun Mediterranean domin neman rayuwa mai kyau a kasashen Turai, abin da ke jawo hasarar rayukansu da dama a kan hanya.

Mr Gideon Chitanga ya kara da cewa, batun tsaro da zaman lafiya ya kamata a kara mai da hankali a kai sosai lokacin taron, musamman ma idan aka yi la'akari da yanayin da ake fuskanta yanzu na Boko Haram a yammacin Afrika da Al-Shabaab a Somaliya a gabashin Afrikan.

Masanin ya kuma bukaci kungiyar ta AU da ta yi aiki tukuru don hadin kai na yankuna yadda za'a iya daidaita nahiyar baki daya, maimakon a rika shiga cikin ayyukan kasuwanci a matsayin kasa daban daban, domin yana da imanin cewa, idan aiki a matsayi kasa kadai na daga cikin abin da yake ta kara kawo koma bayan nahiyar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China