A yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa, Geng Yansheng ya bayyana yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru cewa, kamar yadda kasashen duniya suke fuskanta, kasar Sin ma na fuskantar matsalar hare-hare kan internet, kuma tana daya daga cikin kasashen da aka fi satar shiga yanar gizonsu a duniya. Daga lokacin da aka kafa tashar internet ta ma'aikatar tsaron kasar Sin da ta sojan kasar Sin har zuwa yanzu, an sha kai musu hari, musamman ma a shekarun da suka wuce, yawan hare-haren da aka kai musu ya karu. A shekarar 2012 da ta gabata, matsakaicin hare-haren da aka kai wa wadannan tashoshin internet mallakar sojan kasar Sin daga ketare ya wuce sau dubu 144 a ko wane wata, a ciki kuma yadda aka yi kokarin satar bayanai daga kasar Amurka ya kai kashi 62.9 cikin dari.
Kwanan baya, wani kamfanin Amurka ya ba da wani rahoton cewa, bangaren sojan kasar Sin yana da hannu cikin hare-haren da aka kai wa yanar gizon kasashen Amurka, Canada, Birtaniya da Faransa. Dangane da lamarin, Geng Yansheng ya jaddada cewa, kasar Sin ta mayar da martani kan lamarin. Kamfanin bai fitar da rahoton bisa hakikanin yanayi kuma yadda ya kamata ba. Ya kara da cewa, kasar Sin ta hana masu satar shiga yanar gizo su kai hari da kokarin satar bayanai. Har kullum gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan yaki da laifuffukan da abin ya shafa, haka kuma, bangaren sojan kasar Sin bai taba shiga aikace-aikacen satar shiga yanar gizo ba.(Tasallah)