Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa ta bakin kakakinsa a jiya Litinin, inda ya yi Allah wadai da farmakin boma-bomai da aka kai a Ndjamena, babban birnin kasar Chadi, tare da aika sakon ta'aziyya ga gwamnatin kasar da kuma jama'arta.
Sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya yaba a kan rawar da kasar Chadi ta taka wajen yaki da kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasashen yammaci da kuma tsakiyar Afrika su karfafa hadin gwiwarsu da kafa hadaddiyar rundunar soja wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Kazalika, Ban Ki-Moon ya nanata cewa, ya kamata kasashe daban daban su bi dokokin jin kai da na hakkin dan Adam da kuma na 'yan gudun hijira na duniya a yayin da suke yaki da kungiyar.(Lami)