in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ciwon tarin fukka na hadabar al'ummar Chadi
2015-03-25 14:34:32 cri

Gwamnatin kasar Chadi, tare da taimakon kungiyoyin ba da tallafi, ta ba da bincike da jinya ga masu fama da ciwon tarin fukka a cikin asibitoci ba tare biyan kudi ba, amma duk da haka, wannan cuta na kasancewa har yanzu daya daga cikin manyan cututtukan da ke hadabar al'ummar kasar Chadi, in ji sakataren kasa a fannin kiwon lafiya na kasar Chadi, mista Assane Ngueadoum a ranar Talata.

Bisa kididdigar hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO), a kasar Chadi, ya zuwa shekarar 2014, akwai mutane dubu 20 da ke fama da wannan cuta, amma tsarin kiwon lafiyar kasar ya kasa bincike da kuma ba da jinya ga mutane 12.325 da ke cikinsu, in ji mista Ngueadoum a yayin bikin ranar yaki da ciwon tarin fukka ta kasa da kasa.

A cewar wasu alkaluma na ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Chadi, yawan marasa lafiya da aka gano kuma aka kula da su ya wuce daga 6.200 zuwa 12.325 tsakanin shekarar 2007 zuwa shekarar 2014, adadin nasarar da aka cimma na kulawa da marasa lafiya ya wuce kashi 22 cikin 100 zuwa 72 cikin 100.

A cewar WHO, a shekarar 2013, an kiyasta cewa, sabbin mutanen dake dauke ciwon sun kai miliyan 9 a duniya, amma duk da haka hanyoyi da tsare tsaren kiwon lafiya ba su gano ko kula da kimanin mutane miliyan 6.

Dalilin haka ne, ake gudanar da bikin ranar yaki da ciwon tarin fukka ta kasa da kasa a ko wace shekara bisa taken "kokarin kai ga mutane miliyan 3 masu fama da ciwon tarin fukka a duniya da tsarin kiwon lafiya bai kai gare su ba, domin ba su jinya da kulawa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China