in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Chadi da Ghana na tattauna batun yaki da Boko Haram
2015-03-19 09:39:07 cri

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno ya isa kasar Ghana a ranar Laraba domin tattaunawa tare da takwaransa na kasar Ghana John Dramani Mahama kan batutuwan da ke da nasaba da tsaro a shiyyar yammacin Afrika da kuma tsakiya.

Batutuwan za su mai da hankali musammun ma kan yaki da mayakan kungiyar Boko Haram, in ji wani kwamitin tuntubar juna dake fadar shugaban kasar Ghana.

Ziyarar mista Deby, wanda kuma shi ne shugaban gamayyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika (CEEAC), ta kasance ci gaban zaman taron watan da ya gabata ne tsakanin shi da mista Mahama, da shugaban kasar Guinea-Equatoriale Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, da kuma shugaban kasar Congo Sassou-N'Guesso.

Kasar Chadi na daya daga cikin kasashe biyar na Afrika da kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta dora ma nauyin yaki da kungiyar Boko Haram a Najeriya, da ma wasu kasashen yammacin Afrika da na tsakiya.

Sauran su ne Kamaru, Nijar, Benin da Nijeriya da suka samu babban ci gaba sosai wajen yaki da mayakan dake kaifin kishin islama tun lokacin kiran kungiyar tarayyar Afrika (AU). (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China