Kwamishinan kungiyar tarayyar Afrika kan zaman lafiya da tsaro, Ismail Chergui ya kaddamar a ranar Litinin a birnin N'Djamena na kasar Chadi da bikin kafa rundunar hadin gwiwa ta kwamitin tafkin Chadi (CBLT) bisa tsarin yaki da kungiyar Boko Haram ta Najeriya.
Kasashen Kamaru, Nijar, Najeriya da Chadi, dukkansu mambobin kungiyar CBLT, tare da kasar Benin suka kafa wannan rundunar hadin gwiwa, wadda ake fatan za ta tattara sojoji 8700 da za su kuma kasancewa a karkashin ikon shugaban rundunar sojojin saman Najeriya. Hedkwatar wannan rudunar hadin gwiwa a kafa ta a birnin N'Djamena, kamar yadda ministocin harkokin waje da tsaron kasashen CBLT suka tsai da a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2015. (Maman Ada)