Yan Nigeriya dake zaune a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi sun hada gangami na lumana a Talata domin nuna goyon bayansu ga rundunar hadin gwiwa ta sojojin Chadi da Kamaru domin yaki da kungiyar Boko Haram.
Sun taka tun daga ofishin jakadancin Nigeriya zuwa ma'aikatar tsaron kasar Chadin mai tazaran kilomita 10, inda daruruwan 'yan Nigeriyan suka bayyana hadin kansu wajen yakar ta'addancin kungiyar ta Boko Haram, tare da nuna goyon bayansu ga sojin kasar Chadi 100 bisa 100.
Haka kuma 'yan Nigeriyan sun ba da gudunmuwar abinci ga sojojin Chadi da a yanzu haka suke yakar kungiyar ta Boko Haram.
Mai magana a madadin 'yan Nigeriyan lokacin wannan gangami, Unuoha Micheal ya ce, abin da suka yi kadan ne daga cikin yadda suke goyon bayan mahukuntar Chadi a kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya a kasarsu da yankin baki daya. (Fatimah)