Masu ruwa da tsari da ke halartar taron bitar yini biyu kan irin rawar da kafofin watsa labarai suka taka kan zabukan kasar na shekara 2015 ne suka bayyana hakan a birnin Lagos.
Sun kuma bayyana irin gagarumar rawar da na'urar tantance katunan masu zabe ta taka a zabukan kasar da suka gabata. Sannan suka shawarci hukumar ta INEC da ta rika raba katunan zabe a kan lokaci don ganin an kai ga mutanen da ke zaune a yankunan karkara.
Sanarwar bayan taron ta kuma shawarci INEC kan ci gaba da aikin wasu daga cikin muhimman ma'aikatan hukumar, da samar da isassun kudaden don ilimantar da jama'a game da harkokin zabe.
Taron da ya gudana daga ranar 9 zuwa 10 ga watan Yunin wannan shekara, ya samu halartar hukumomi da kungiyoyin kula da harkokin watsa labarai, kungiyoyi masu zaman kansu, masu rajin kare nuna bambancin jinsi da sauran abokan hulda na kasa da kasa. (Ibrahim)