Ban Ki-moon ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, MDD ta kafa tawagogin kiyaye zaman lafiya 71, kuma ma'aikata fiye da miliyan daya sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya don taimakwa kasashen duniya samun 'yanci kansu, taimakawa zaben shugabannin kasashe, tabbatar da tsaron fararen hula, kwace makamai daga hannun dakaru fiye da dubu 100, tsara dokoki, tabbatar da hakkin dan Adam, samar da sharadi don sa kaimi ga 'yan gudun hijira da su koma gida.
Hakazalika kuma, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, aikin kiyaye zaman lafiya na MDD bai biya bukatun kiyaye zaman lafiya a duniya ba. Ya ce, ana bukatar Karin kudi, da horaswa da kuma na'urori masu inganci. Kana ana bukatar kasashe masu ci gaba da su bada taimako, kana suma kasashe membobin MDD an bukace su da su kara nuna goyon baya ga MDD a fannonin tattara kudi, da tura sojoji. (Zainab)