Kwalejin nazarin fasahohin aikin gona ta nan kasar Sin ta fidda wani bayani dake cewa, sabbin fasahohin aikin gona sun ba da gudunmawa kwarai ga ci gaban aikin gona da kashi 56 cikin dari. Kana fasahohin sun ba da matukar taimako wajen samun bunkasuwa ta fuskar samar da abinci cikin shekaru 11 a jere.
Mataimakin ministan aikin gona kuma shugaban kwalejin kimiyya da fasahohin aikin gona na kasar Sin Li Jiayang, ya bayyana cewa, a bana kwalejin na kokarin bunkasa fasahohi, da kimiyya, dangane da wasu nau'o'in abinci da ake shuka su, ciki hadda shinkafa, da masara, da alkama, da wake da bado da sauransu.
Masu nazarin kimiyyar su kimanin 2000 ne suka gudanar da hadin kai wajen gabatar da sakamakon nasu. (Amina)