in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba ta goyon amfani da siyasa wajen yayata batun kare hakkin bil-adama
2014-12-19 20:20:55 cri
Kasar Sin ta ce ba ta goyon bayan yadda wasu kasashe ke amfani da batun kare hakkin bil-adam wajen tursasawa wasu kasashe ba.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne ya bayyana hakan yau yayin taron manema a nan birnin Beijing, bayan da kudurin babban taron MDD ya nemi a gabatar da kasar Koriya ta arewa gaban kotun hukunta manya lafiffuka ta duniya ICC kan yadda take tafiyar da harkokinta na kare hakkin bil-adam

Ya ce, har kullum kasar Sin na goyon bayan amfani da yin shawarwari da hadin gwiwa wajen warware bambance-bambance da suka shafi batun kare hakkin bil-adam. Sannan ba ta goyi bayan yadda ake amfani da siyasa wajen ruruta wannan batu ba.

Mr Qin Gang ya ce, kwamitin sulhu na MDD ba wuri ne da ya dace wajen tattauna batun kare hakkin bil-adama ko gabatar da wannan batu ga kotun ICC don warware wannan matsala ba.

A ranar Alhamis ne babban taron MDD ya kada kuri'ar amincewa da kudurin da kungiyar EU da Japan suka gabatar don gabatar da kasar Koriya ta arewa a gaban kotun na ICC. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China