Ranar 10 ga wata rana ce ta hakkin bil'adam ta duniya. A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana a birnin Beijing, Hong Lei ya bayyana cewa, Sin tana sanya matukar muhimmanci kan kiyaye ikon rayuwa da na ci gaba na jama'ar kasar da yawansu ya kai kimanin biliyan 1.3.
Yace hakan ya sa kasar take kokarin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, don haka rayuwar jama'ar kasar ta sami kyautatuwa sosai.
Hong Lei ya bayyana cewa, bama kawai Sin tana dora muhimmanci kan kyautata hakkin bil'adam a kasar ba, har ma ta na hadin gwiwa da sauran kasashen duniya cikin yakini bisa manufar girmama juna da zaman daidai wa daida, tare da kara yin shawarwari da mu'amala domin samun fahimtar juna, da kawar da sabanin ra'ayi. Dadin dadawa, Sin tana kokarin sa hannu cikin aikin kiyaye hakkin bil'adam na MDD, kuma bata amince da a mayar da batun hakkin bil'adam a siyasance ba, ko nuna bambanci a kan batun, kasar ta ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar sha'anin hakkin bil'adam na duniya.(Fatima)