in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta aike da sojojin wanzar da zaman lafiya a Darfur
2014-08-19 20:27:29 cri
A yau Talata 19 ga wata Jami'an tsaro 105 ne da suka kunshi sojoji da ma'aikata suka bar birnin Ji'nan dake gabashin Kasar Sin zuwa Darfur na kasar Sudan don gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya,kamar yadda majiyar Sojojin kasar ta sanar.

Masu aikin wanzar da zaman lafiyan da suke cikin koshin lafiya da karfin jikin su 225 zasu gina filin saukan jiragen sama,gadoji da hanyoyi sannan su samar da ayyukan jinya ma mazauna wannan wuri.

Tawagar sun riga sun samu horo a harshen Ingilishi,ka'idojin MDD da kuma a kan yanayin rayuwar mutanen da zasu iske a inda zasu.

Wani tawagar na biyu da ya kunshi sojoji 120 da jami'ai zai tashi a ranar 27 ga watan nan da muke ciki.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China