in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da harin da aka kai ma sojojin wanzar da zaman lafiya a Darfur ta Sudan
2013-04-20 16:06:32 cri
Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi sanarwa ta bakin kakakinsa a ranar 19 ga wata, inda ya yi Allah wadai da harin da aka kai ma sojojin wanzar da lafiya na majalisar dake yankin Darfur na kasar Sudan a waccan rana.

Cikin sanarwar an bayyana cewa, wasu dakarun da ba a san asalinsu ba sun kai hari a ranar 19 ga wata, a sansanin rundunar sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da kungiyar kasashen Afirka AU (UNAMID) dake jihar Darfur ta gabas, inda lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani sojan Najeriya, da raunatar da wasu guda 2. Ban Ki-moon ya nuna mamaki da kuma juyayi dangane da lamarin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China